WAYE ADOLF HITLER?

Adolf Hitler haifaffen Dan qasar (AUSTRIA) Mu kula akwai babanci tsakanin qasar AUSTRIA da AUSTRALIA. Qasar AUSTRIA wata qaramar qasa ce dake makwaftaka da Qasar GERMANY dake turai. An haife Adolf Hitler a shekarar “1889” Adolf Hitler tun Yana qarami ya rasa iyayen sa yayi rayuwar maraici Kuma yasha wahalar rayuwa,  Hitler mutum ne Mai baiwar Zane-zane (Arts)  Kuma mutum ne Mai son Tarihi, ya taso Kuma ya Girma acikin qasar sa ta haihuwa AUSTRIA Mai makwaftaka da GERMANY, mutun ne Mai Qin Jinin Yahudawa Kuma Yan tuhumar shugabannin Turai da Daure ma yahudawa suna juya turai da qasashen su na Gado yadda suke so! Tare da zargin shugabanni da fifita yahudawa Akan “Yan Asalin qasashen su, loqacin da wannan ra’ayin ya fara bayyana ga wannan matashin mutun Sai aka daqile yunkurin sa na shiga Aikin soja Kuma aka rufe Shi a gidan yari tsawon loqaci, Bayan fitowar sa Sai ya wallafa wani littafi Mai suna (MY STRUGGLE}  Ma’ana GWAGWARMAYA TA. 

Daga nan Bayan rashin samun cikakkiyar dama daga Qasar sa ta AUSTRIA Sai ya yanke shawarar yaga Indigent nashi na qasar ya Koma qasar GERMANY Mai makwaftaka da AUSTRIA Wanda Hitler yayi imanin cewa qasar Germany ma qasar su ce ta Gado Domin ma kusan Harshen su daya Kuma Al’adun su daya Qasar Germany ta karbi baquncin matashi Hitler ya zama Dan qasa ya samu sabon (NATIONALITY)  Wanda yayi Hakane a shekarar 1913 ana saura shekara daya a fara Gwabza yaqin DUNIYA na farko (WWI}  nan take Hitler ya shiga Aikin soja Amma cikin Volunteer ma’ana Sojan Sakai.

Mu haɗu a rubutu na biyu

✍️ Abbas Ibrahim Zauma
#Spaddaawah

KA NEMI YARDAR IYAYE DAN KA SAMI YARDAR ALLAH.

Allah (S.W.T) Ya wajabta a kan ɗa da ya ciyar da iyayensa, don su ɗanɗani zaƙin wahalar da suka yi, kuma ya sa al’amarin ga iyayen daidai samari ne, ko tsofaffi ne, masu hali ne ko talakawa ne. Game da ciyarwa ya ce:-

Daga Ɗan Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya ce:- “Babu daga musulmi da yake da iyaye biyu musulmi, ya wayi gari yana mai nema masu abin da zasu ci har sai Allah ya buɗe masa ƙofofi biyu na Aljannah. In ko Uba ne kawai ko Uwa kawai ƙofa ɗaya in kuma Uba ya yi fushi da shi ko Uwa tayi fushi dashi, Allaj ba zai yarda dashi ba, har sai iyayen sun yarda dashi, sai aka ce ko su iyayen ne suka cuceshi, sai aka ce, ko sun cuceshi!”.

A nan nake jan hankalinmu, mu masu iyaye da muke cikin hatsari Allah ne zai fiddamu; amma fa sai mun bi iyaye. Wannan hadisi yana nuna mana yadda aka hori ɗa da ya fita ko ina ne ya nemo abin da zai ciyar da iyayensa komai wahala. Allah zai yi masa tukwicin Aljannah, kuma ya yarda da shi, ɓatawa iyaye rai kuma yana wajabta fushin Allah da toshe rahamarsa, komai matsayin ɗan.

ROƘON ALLAH TA’ALA DA SAKANKANCEWA.

Manzon Allah (ﷺ) yace: “Ku roƙi Allah kuna masu sakankancewa da amsawa”.

Wannan Hadisi yana koya mana mahimmacin roƙon Allah ta’ala da kuma sakin jiki da cewa Allah zai amsa addu’a ba tare da kokwanto ba. Allah yana da kirki, Allah mawadacine, Allah bashi da rowa, Allah yana jinka, Allah yana ganinka, Allah yasan halin da kake ciki. Allah ka Amsa buƙatarmu ka yaye damuwarmu.

MUHIMMANCIN TAIMAKON MARAYU

Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.

Tsoron Allah shi ke bada zaman lafiya amma da yake masu imani suke temakawa marayu se aka gano zaman lafiya na nan zinƙir a temakawa marayu kamar yanda aka bayyana.

Misali kamar duk wanda yaga anyi mutuwa marayun da aka bari suna samun kulawar gaske daga al’umar Annabi (ﷺ) to bazai ji tsoron mutuwa akan gaskiya da ɗaukaka Addinin musulunci ba, bugu da ƙari bazai sace kuɗaɗen al’umma ba dan tarawa ƴaƴansa ba don yaga yadda marayu suke samun kulawa.

Kaga kenan waɗanda suke kwashe kuɗin al’umma don su tarawa ƴaƴansu zasu ragu. masu ɓoye dukiyarsu domin su taskacewa ƴaƴansu zasu ragu. wanda hakan ze kawo raguwar masu shiga wuta.

✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
10 Jumada Sani 1444 AH
03 January 2023 M

HAƊARIN DAKE CIKIN KAƊAITAR NAMIJI DA MACE.

Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.

Itade kaɗaita da ƴa mace se kai se ita wacce ba matarka ba kuma akwai aure tsakaninku da ita abune me hadari a addinin musulunci. wannan ce tasa fiyayyen me ƙaunarmu ɗan gata Allah wanda ba’a taɓa kamarsa ba kuma baza’ayiba Annabi Muhammad (ﷺ) yace: “kadda wani mutum ya kaɗaita da mace se tare da muharraminta, wato wanda babu aure a tsakaninsu” Imamul Muslim ne da Bukari suka rawaito Hadisin. wanda aka karɓoshi daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhuma).

Wajibine mubi umarni na Annabi (ﷺ) kadda mace da namiji su keɓe a yanayin zance na zawarawanmu ko ƴan matanmu da ke gidajenmu ko duk wata mu’amala da tasa se namiji da mace sun haɗu don kaucewa afkuwar zina. Mu Sani dukkan zinar da take faruwa idan kabi a hankali zakaga bata faruwa se da Namiji da mace suka keɓe a inda babu me ganinsu.

✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
09 Jumada Sani 1444 AH
02 January 2023 M

NASIHA

‘Yan uwa mu kula; kadda muje muna aibata ‘yan uwanmu musulmi tare da bayyana laifukansa ga jama’a domin samun wani sabani musanman na siyasa ko kuma bangarancin addini, domin kare mutuncin wani daban wadda ba lalle yasan da zamanka ba ko kuma wata fahimta wadda ba lalle kaidin kana kan dai-dai ba.

Hanyar Isar da sako wadda jama’a kake so su fuskanceka hanyace ta lafazi me kyau da bayyana manufofi idan a siyasance Ne idan kuwa a addinance Ne to wannan kam magana ce ta hujja da ilimi mabayyani. Domin kuwa duk Wanda zaka isarma da sako inde so kake ya fahimceka to hakika ba cin nasara bane idan ka biyo ta hanyar cin mutuncinsa ko kuma wani nashi. Memakon ya fahimci sakon sede ya kara tunzuruwa tare da kara sabunta wani sabanin.

Lokaci yayi Wanda ya kamata duk me hankali ya nutsu yasan mutuncin kansa, musanman a wannan lokaci da Muke ciki Wanda mafi yawa daga cikin makiyanmu suke amfani da rabuwar kanmu wajen cimma tasu nasarar. Idan ya kasance kanmu a hade yake shine zamuci nasarar amma idan kowa yace sede a bishi, shine akan gaskiya to a dai-dai wannan lokaci shine Muke akan bata.

Ina rokon Allah ya kara hada kan musulmi da kuma ‘yan arewa, ya Allah ka bamu ikon sanin ciwon kanmu ko shuwagabanninmu sunji tausayinmu. Domin idan bamasan junanmu to kuwa zamu Dade a wahale. Allah ya kiyaye.