GABATARWA.
Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta kuma cikamakin manzanni. shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da Alayensa da sahabbansa tare da mabiya sunnah tasa, har zuwa ranar ƙarshe.
Bayan haka jama’ar musulmi ina mai farin cikin gabatar muku da wannan littafi mai albarka, wato me suna “FALALAR BIN IYAYE DA HATSARIN SAƁA MUSU” wallafar Babban Malami Sheikh Tijjani Bala ƙalarawi wanda ni Muhammad Abdulrahman Rano ɗan ƙaramin ɗalibi nake rubutawa a kafafen sadarwa.
Malam ya cigaba da cewa: Ban fassara waɗannan hadisai ba sai bayan nayi zurfin tinani a kaina da jama’ar musulmi masu yawa, waɗanda ƴaƴansu suke kyautata musu, kuma na sadu da wasu jama’a da dama a wasu jihohin Nijeriya masu kwatanta biyayya ga iyayensu, da irin fa’idar da suke gani sakamakon biyayya. haka ma na sadu da waɗanda suka guje wa iyayensu don basu da hali, suka maida kawunansu ƴaƴan wasu masu hali, suka cigaba da bautawa wasu ƙarti bauta marar lada! babu ko godiya, ga kuma rashin albarka cikin duk abinda suka samu.
Ji da gani na irin waɗannan haɗarori da muka shiga, shi yasa na rubuta wannan littafi, ko Allah (S.W.T) ya tsame wadanda suke saɓa wa iyayensu daga halaka zuwa tsira, kuma ya amfani manya, waɗanda ko dai sun saɓawa iyayensu a baya kuma iyayen sun mutu ba su shiriya ba, ko kuma iyayen suna da rai amma babu jituwa tsakaninsu, wato basa ganin girman iyayen, da fatan za su yi ƙoƙarin kyautatawa iyayensu saboda su samu rayuwa mai albarka duniya da lahira.
RASHIN TARBIYYA DA RASHIN TSAWATAWA.
Wani lokaci ba banza ba za ka ga raini ya shiga tsakanin iyaye da ƴaƴa, ko da yake ba hujjah bace. Amma idan aka duba yadda ake aure barkatai kuma da yadda yara suke ganin iyayensu na dukan iyayensu mata, ko kuma yadda iyaye mata kan cukume rigar miji tqnq ɗura masa zagi; kai harma wani lokaci zakaga yadda salacin uba kan haifar da ƴaƴan kishiya su yi wa matar ubansu duka, ko kuma wasu iyaye maza da kan aikata wasu munanan halaye a gaban ƴaƴansu.
Wasu iyayen ƴaƴansu na sa ne da irin ɓarnar da suke shukawa, kamar ajiye matan banza a wasu wurare na musanman, ko kama musu gidaje don zaman tare ba bisa sunnar Annabi ba, ko shaye – shaye ko aikata wasu miyagun laifuka; wanda haƙiƙa yana haifar da raini tsakanin iyaye da ƴaƴa. Amma fa uwa da uba komai suke ba hujja bace a ce ƴaƴansu su raina su biyayyar su daban tsakaninsu da iyayensu, wadda Allah ya wajabta musu amma a nan ina nuna wa iyayene kada su riƙa yin abin da zai jawo raini tsakaninsu da da ƴaƴansu.
Haka ma lallai iyaye su ga cewa ƴaƴansu sun rungumi sallah a kan lokaci saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) inda yace; “ku hori ƴaƴanku da sallah sune shekara bakwai, ku buge su in sun kai goma, amma ba bugu mai fasa jiki ba, wato in sunƙi sallah. kuma ku raba tsakaninsu wajen kwanciya”. Sau dayawa wasu iyaye ba sa son a faɗi laifin ƴaƴansu wai saboda soyayya. kuma bazasu iya yi musu faɗaba wani lokaci kuma sau dayawa ƴaƴa su yi aikin ashsha wai sai kaji uba yana cewa in ka ƙi dainawa zan gaya wa Hajiya don nasan kafi tsoranta.
Wani uban abin kunya idan akace ana son ƴarsa da aure sai kaji yace se abinda Hajiya tace. Kuma lallai ya kamata uba ya sa ido akan karatun ƴaƴansa, biyan kuɗin makaranta. bayan ciyarwa da shayarwa da tufatarwa tare da tsawatarwa, da sa ido akan abokan ƴaƴansa ko ƙawayen ƴarsa: saboda gudun ɗaukar mummunar ɗabi’a.
Haka ma ya zama wajibi iyaye musanman uba, su sa ido game da zuwa biki da liyafar aure da shaƙiyai kan shirya bayan ɗaurin aure. domin yanzu abun ya ƙazanta da gaske, matuƙar iyaye suka bar ƴaƴansu ba sa sa ido to duk abinda ya faru kar suyi kuka da kowa sai kansu. Hakanan kar iyaye su sa san duniya a zuciyarsu saboda kawwai sunada kyakyawar ƴa, ko kuma suna ganin su ƴan dangi ne, ko kuma me neman ƴarsu su me da shi ba komai ba saboda shi ba wane bane ba kuma ɗan wane bane.
Kai harma sai kaga yarinta ta bijirewa iyayenta saboda kawai wai sun matsa mata. haka ma yana da kyau iyaye su nisanta ƴaƴansu daga kallon fina – finai na batsa dan shima yana jawo raina magabata saboda sharrin da abin yake haifarwa. hakama kadda iyaye suyi shiru yayin da sukaga wani marar hankali shashasha, ɗan shaye -shaye, ɓarawo ko me neman mata ta baya yana son ƴarsu suyi shiru kawwai wai saboda ze basu abin duniya.
YADDA WASU SUKA MAIDA ƳAN UBA
Ba ƙaramin sharri ba ne a ce iyaye su zura ido su ga ƴaƴansu maza da mata ba su jituwa, haka kawai. wai saboda ubansu ɗaya maimakon suyi zumunci na ƴan uwantaka irin wanda Allah da manzonsa suke so. sai su ɗauki wata baƙar gaba, kai kace gabar musulmi ce da kafiri a wajen yaƙi. kuma wai har sai kaji ana cewa ƴan uba ai daga Annabi Yusuf (A.S) aka samo. To, wannan ba ƙaramar ƙarya bace.
Ƙissar Annabi Yusuf (A.S) tana da hikimomi da yawa, ba labarin haɗa rigima take ba, ba kuma koyar da rigima take ba, maimakon haka tana ma ƙara haɗa zumunci, tare da ƴan uwa da soyayya da yafewa, da nemawa juna rahamar Allah, tare da girmama mahaifi da neman addu’arsa mai albarka. da kuma matso da ƴan uwa kusa, su ma suci arziki yayin da ɗan uwansu Allah ya yi masa wata ni’ima.
Domin a yanzu an kusa, ko kuma an wayi gari ƙani baya ganin girman wansa, sai in yanada kuɗi koda kuwa uwa ɗaya uba ɗayane. balle kuma ace uba ɗayane, haka ta kai ɗan wa baya ganin girman ƙanin ubansa ko wan ubansa tana yiwuwa ma suna gari ɗaya baya gaisheshi. sai anyi mutuwa su haɗu, ko kuma wajen ɗaurin Aure, daga nan kuma sai wani lokaci.
A nan ya kamata in jinjina wa mata masu zumunci, su ma ba duka ba. domin zumuncin mata ba kamar maza ba, wajen ziyara, suna, biki, tare da ciyarwa. Sai fa wadda shaiɗan yayi mata huɗuba ta kauce. Ya kamata in jawo hankalin ɗan uwa wanda Allah (S.W.T) ya yi wa baiwa ta kuɗi, amma ƴaƴansa basu dashi. To ya ji tsoron Allah kadda ya maida ƴaƴansa ba komai ba, saboda kawai ya fi su abin hannu; ya riƙa wulaƙanta su.
BIYAYYA GA IYAYE.
Mai yiwuwa ma ya barsu a ƙauye, ya shigo birni. Wani ma ba ya so a same shi cikin abokansa a ce masa ga ƴan uwan babanka nan, ko na babarka sunzo. sai ya canza fuska, wai zasu kunyata shi cikin abokansa. Ya kamata duk mai hankali ya yi ƙoƙarin kyautata zumunci tsakaninsa da ƴan uwan mahaifiya tasa, da mahaifinsa. Kuma ya kula da zumuntar ƴaƴan ƴan uwansa maza da mata ya riƙa ziyartasu. yana yi musu aike a kai a kai in mabuƙata ne.
Kuma koda ba mabuƙata ba ne ya wajaba a kyautata musu koda ta hanyar wasiƙa, ko saƙon baka. Kuma yayi iya ƙoƙarinsa ya ga tarbiyar ƴan uwansa ta yi kyau, yaga ya rabasu da shaye shayen miyagun ƙwayoyi. Kar yace bashi ya haife su ba, ko kuma ba uwa ɗaya uba ɗaya suke ba. A’a ya kamata ya sowa ƴan uwansa alkairi ya kuma ƙi musu sharri, kamar yadda yake yiwa kansa. Kuma ya wajaba ka zama mutumin kirki a cikinsu.
Cikin Alƙur’ani mai girma, akwai ayoyi masu kira zuwa bautar Allah shi kaɗai amma a haɗe da kyautata wa iyaye, daga cikinsu akwai inda Allah (S.W.T) Yake cewa:
“Ku bautawa Allah kada ku hada wani da Allah kuma ku kyautata ga iyaye”.
Suratun: Nisa’i, Ayah: (36).
A nan Allah (S.W.T) Ya nuna mana ibada ba ta karɓuwa sai da biyayya ga iyaye, shi ya sa Manzon Allah (S.A.W) ya ce a cikin Hadisin da Amru ɗan Aljuhani ya ce:
Haƙiƙa wani mutum yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ya Manzon Allah (S.A.W) na shaida haƙiƙa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma kai Manzon Allah ne. Na yi salloli biyar na ba da zakkar dukiyata, na yi Azumin watan Ramadan. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce wanda duk ya mutu a kan wannan yana tare da Annabawa, da Siddiƙai da shahidai ranar Alƙiyamah. Haka sai Annabi ya haɗa yatsun sa biyu kuma ya ce matuƙar bai saɓa wa iyayensa ba. (Imamu Ahmad da Ɗabarani suka rawaito da dangane mai kyau).
Wannan Hadisi yana nuna mana duk biyayyar da za ka yi wa Allah (S.W.T) ba za ka sami amfaninta ba matuƙar kana saɓa wa iyayenka. Haka ma babu yadda imani zai zauna a zuciya matuƙar ana saɓa wa iyaye, kuma su iyayen fa ba lalle ne su zama Musulmi ba, sai fa in sun neme ka ne da saɓawa Allah (S.W.T) to anan ba za ka bi su ba.
Akwai ayoyi a cikin Alƙur’ani mai girma waɗanda suke nuna mana haɗuwar ibadah wadda babu damu ayi amfani da ɗaya a bar ɗaya, kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce a cikin suratul Baƙra:-
“Ku tsaida sallah ku bada zakkah”
Suratul Baƙra, Ayah ta: 43.
A Nan tsai da Sallah da bada zakkah rukunai ne, biyu cikin rukunan musulunci da aka gina musuluncin a kai, saboda haka babu dama kace kana da imani , zakayi sallah amma bazaka bada zakkah ba, bayan kuwa kana da hali. Kamar yadda aiki mai kyau ba zai karɓu ba sai da imani, aiki mai kyau yana sanya yardar Allah. Allah (S.W.T) Ya ce:-
“Waɗanda suka yi imani suka yi aiki mai kyau za mu shigar da su cikin mutanan kirki”.
Suratul Ankabut, Ayah ta: 9.
Ga kuma wani Hadisi mai kama da wannan daga babban sahabi;
An ruwaito daga Ɗan Abbas (R.A) yace:- Ayoyi uku suka haɗe da Abu uku, Ɗaya ba za ta karɓu ba sai da ƴar uwarta. Faɗin Allah (S.W.T) “ku yi biyayya ga Allah ku yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W), duk wanda yai biyayya ga Allah bai yi biyayya ga Manzon Allah (S.A.W) ba, ba za’a karɓa ba. Na biyu ku tsaida sallah ku bada zakkah, wanda yai sallah bai ba da zakkah ba ba za’a karɓi sallarsa ba. Na uku faɗin Allah (S.W.T) Ka gode min da iyayenka, wanda ya godewa Allah bai godewa iyayensa ba, ba za’a karɓa ba”. “KITABUL-KABA’IR”
Bin iyaye tare da kyautata musu ba sabon abu ba ne, tun kafin bayyanar Annabi Muhammad (S.A.W) ake horan al’ummomi da biyayya ga iyayensu har zuwa zamanin Manzon Allah (S.A.W), Kamar yadda Allah (S.W.T) Ya ce:-
“Yayin da muka riƙi alƙawari ga bani Isra’ila cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyayenku ku zama ma su biyayya a garesu”.
Suratul Baƙra, Ayah: 83.
Wani alƙawari da bani Isra’ila suka yanka wa kansu suka gabatar da shi gaban Allah (S.W.T) cewa zasu bauta masa ba za su yi tarayya da shi ba, kuma zasu zama masu biyayya ga iyayensu, ba za su yi jayyaya da falalar iyayensu ba, kuma zasu yi alƙawari ga makusantansu kuma zasu kyautatawa marayu da talakawa. Sai suka warware alƙawarin sai Allah yayi fushi dasu.
Duk ɗan kirki mai biyayya ga iyayensa zai so ya ji yadda Allah (S.W.T) ya yabi manyan Annabawansa saboda biyayya ga iyayensu tare da cewa zaɓaɓɓunsa ne a cikin hallittarsa amma saboda muhimmancin kyautatawa iyayen, Allah ya yabesu.
Karanta ayoyin Allah (S.W.T) da ya yabi Annabi Yahaya Amincin Allah ya ƙara tabbata a gareshi, inda yake kyautatawa iyayensa, tare da manyanta da suka yi, bai bar su ba duk kuwa da matsayinsa a wajen Allah. Allah (S.W.T) Ya ce:-
“Annabi Yahaya mai biyayya ne ga iyayensa bai zama mai girman kai mai saɓo ba”.
Suratuh: Maryam, Ayah: 14.
A nan nake so na ja hankalin mai karatu, mu duba yadda Allah (S.W.T) ya fara yabon Annabi yahaya a kan bin iyayensa. Haka ma Annabi Isa Amincin Allah ya ƙara tabbata a gare shi, cikin baiwar da Allah ya yi masa ya ce:-
“Mai biyayya ne ni ga mahaifiyata, bai sanyani mai fita daga horonsa ba”.
Suratuh: Maryam, Ayah: 32.
Haka yaran kirki masu biyayya za su so su ji yadda Allah (S.W.T) ya yi baiwa ta ɗa mai albarka ga Annabi Ibrahim, Amincin Allah ya tabbata a gareshi. Duk yaran kirki mai biyayya zai yi murna da yadda Annabi Isma’il ya yi, kamar yadda Allah (S.W.T) ya bayyana, Ya ce;-
Annabi Ibrahim Ya ce;- “Ya ɗana ni na gani cikin barci ina yanka ka, sai ka duba mai ka gani? sai nan da nan Annabi Isma’il ya amsa wa mahaifinsa ya ce:- “Ya Babana aikata abinda aka hore ka, za ka same ni in Allah ya so daga masu haƙuri”.
Surah: Safat, Ayah; 102.
Allahu Akbar, kun ji ɗa mai biyayya. Uba ne fa ya ce zai yanka ɗansa, ɗan ya ce yanka ni Baba!
Ina ƴaƴa masu zagin iyayensu, wani ya doki ubansa, wani kuma ya mari ubansa kowanne ɗa ya sani cewa shi fa dashen iyayensa ne kamar yadda mutane suke shuka, in ta girma su yi amfani da ita, haka ma ya kamata kowanne ɗa yayi: ya zama mai biyayya da ladabi da girmama iyayensa, domin sune sababin zuwansa duniya, su suka ɗauki nauyin rayuwarsa, tarbiyarsa, tun yana ciki har Allah ya kawo shi duniya ya rayu ya zama mutum. To a nan inde yana so ya zama me albarka yaya ze yiwa ubansa tsawa, ko ya tozarta shi cikin jama’a, balle a ce ya hana iyayensa abinci, amma ya baiwa matarsa, iyayensa ne fa suka ciyar dashi suka shayar dashi suka bashi sutura har ya girma, su kuma suka fara tsufa suna buƙatar taimakonsa a wannan lokaci, amma abin ya faskara.
DUK ABINDA IYAYE SUKA ƊAUKA CIKIN DUKIYAR ƊANSU YAYI DAI-DAI.
Allah (S.W.T) ya halatta wa iyaye dukiyar ƴaƴansu, Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta rawaito da Annabi (S.A.W) ya ce:- “Haƙiƙa mafi daɗin abinda kuka ci daga nemanku, kuma lallai ƴaƴanku daga nemanku suke”. Wato komai iyaye sukayi da dukiyar ƴaƴansu dai-dai ne domin daga garesu ya fito; su suka shuka shi har ya fito. Saboda haka babu mai hana iyaye kayan ɗansu. shi yasa imamu Ahmad da Hakim suka rawaito cewa:- “Ɗan Mutum yana daga abin nemansa, ku ci daga dukiyoyinsu kuna masu kwanciyar hankali da farin ciki”.