MUHIMMANCIN TAIMAKON MARAYU

Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.

Tsoron Allah shi ke bada zaman lafiya amma da yake masu imani suke temakawa marayu se aka gano zaman lafiya na nan zinƙir a temakawa marayu kamar yanda aka bayyana.

Misali kamar duk wanda yaga anyi mutuwa marayun da aka bari suna samun kulawar gaske daga al’umar Annabi (ﷺ) to bazai ji tsoron mutuwa akan gaskiya da ɗaukaka Addinin musulunci ba, bugu da ƙari bazai sace kuɗaɗen al’umma ba dan tarawa ƴaƴansa ba don yaga yadda marayu suke samun kulawa.

Kaga kenan waɗanda suke kwashe kuɗin al’umma don su tarawa ƴaƴansu zasu ragu. masu ɓoye dukiyarsu domin su taskacewa ƴaƴansu zasu ragu. wanda hakan ze kawo raguwar masu shiga wuta.

✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
10 Jumada Sani 1444 AH
03 January 2023 M

HAƊARIN DAKE CIKIN KAƊAITAR NAMIJI DA MACE.

Daga: Malam Ɗayyabu Umar Memai Rano.

Itade kaɗaita da ƴa mace se kai se ita wacce ba matarka ba kuma akwai aure tsakaninku da ita abune me hadari a addinin musulunci. wannan ce tasa fiyayyen me ƙaunarmu ɗan gata Allah wanda ba’a taɓa kamarsa ba kuma baza’ayiba Annabi Muhammad (ﷺ) yace: “kadda wani mutum ya kaɗaita da mace se tare da muharraminta, wato wanda babu aure a tsakaninsu” Imamul Muslim ne da Bukari suka rawaito Hadisin. wanda aka karɓoshi daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhuma).

Wajibine mubi umarni na Annabi (ﷺ) kadda mace da namiji su keɓe a yanayin zance na zawarawanmu ko ƴan matanmu da ke gidajenmu ko duk wata mu’amala da tasa se namiji da mace sun haɗu don kaucewa afkuwar zina. Mu Sani dukkan zinar da take faruwa idan kabi a hankali zakaga bata faruwa se da Namiji da mace suka keɓe a inda babu me ganinsu.

✍️ Muhammad Abdulrahman Rano
09 Jumada Sani 1444 AH
02 January 2023 M