Allah (S.W.T) Ya wajabta a kan ɗa da ya ciyar da iyayensa, don su ɗanɗani zaƙin wahalar da suka yi, kuma ya sa al’amarin ga iyayen daidai samari ne, ko tsofaffi ne, masu hali ne ko talakawa ne. Game da ciyarwa ya ce:-
Daga Ɗan Abbas Allah ya ƙara masa yarda ya ce:- “Babu daga musulmi da yake da iyaye biyu musulmi, ya wayi gari yana mai nema masu abin da zasu ci har sai Allah ya buɗe masa ƙofofi biyu na Aljannah. In ko Uba ne kawai ko Uwa kawai ƙofa ɗaya in kuma Uba ya yi fushi da shi ko Uwa tayi fushi dashi, Allaj ba zai yarda dashi ba, har sai iyayen sun yarda dashi, sai aka ce ko su iyayen ne suka cuceshi, sai aka ce, ko sun cuceshi!”.
A nan nake jan hankalinmu, mu masu iyaye da muke cikin hatsari Allah ne zai fiddamu; amma fa sai mun bi iyaye. Wannan hadisi yana nuna mana yadda aka hori ɗa da ya fita ko ina ne ya nemo abin da zai ciyar da iyayensa komai wahala. Allah zai yi masa tukwicin Aljannah, kuma ya yarda da shi, ɓatawa iyaye rai kuma yana wajabta fushin Allah da toshe rahamarsa, komai matsayin ɗan.
